IQNA

Makokin shahadar Fatima a hubbaren  Hossaini da Abbasi

15:42 - December 06, 2024
Lambar Labari: 3492331
IQNA - Dubban masu ziyara a Karbala ma'ali ne suka gudanar da zaman makoki a ranar Alhamis 5 ga watan Disamba, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan zagayowar ranar shahadar Sayyida Fatimah Zahra (AS) 'yar Manzon Allah (S.A.W) a hubbaren Husaini da Abbas

Kamar yadda al-Kafil ya bayyana cewa, a jiya Alhamis ne hanyoyin da suka kai ga haramin Imam Hussain (a.s.) da Sayyiduna Abbas (a.s.) da kuma tsoffin mashigai na birnin Karbala sun ga dimbin masu ziyara  daga ciki da wajen kasar Iraki, wadanda suka zo domin yin ziyara da ta'aziyyar shahadar Sayyida Zahra sun kasance a Karbala.

Mahalarta haramin Hosseini da Abbas sun yi makoki baki daya a kan wannan lokaci.

An fara gudanar da wannan taro  ne daga harabar hubbaren Abbas (a.s) inda bayi suka rufe tazarar da ke tsakanin wuraren ibadar da bakin ciki da makoki har suka isa hubbaren Imam Husaini (a.s) kuma a nan ne suka yi jimamin shahadar Sayyidina Zahra (AS).

Haramin Imam Hussaini da wuraren ibada a cikin hubbaren Abbasi sun hada ayyukan hidima domin masu ziyara, ta hanyar samar da tsaro da kiwon lafiya da samar da tsaftataccen abinci da ruwan sha da sauran ayyuka.

A yayin taron shahadar Sayyida Zahra (A.S), masaukin Bakin hubbaren Abbas ya samar da abinci kusan dubu tara ga masu ziyara a Karbala.

Sayyid Alaa Abdul Hossein mataimakin ma'aikacin gidan baki na hubbaren Abbasi ya bayyana cewa: Ma'aikatan gidan baki sun gudanar da ayyuka na musamman domin tunawa da zagayowar ranar shahadar Sayyida Fatima Zahra (AS) tare da raba abinci ga maziyarta  a wurare da dama.

Ya kara da cewa: An bude wata cibiyar rarraba kayayyakin abinci a wajen haramin, kusa da kofar Bagadaza, an kuma raba abincin rana da abincin dare 5,000 ga maziyarta.

 

 

4252552

 

 

captcha